You are currently viewing SHIN ALLAH NA ‘BOYE AIKINSA?

SHIN ALLAH NA ‘BOYE AIKINSA?

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI

 إِنَّ السَّاعَةَ آتِيَةٌ أَكَادُ أُخْفِيهَا لِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍ بِمَا تَسْعَىٰ

ALLAH (S.W.T) Yana fada a cikin littafinSA Mai tsarki, surar ‘DAHA, aya ta 15, cewa:

{“Hakika alkiyama za ta zo, ina nufin ‘boye ta ne don a saka wa kowanne rai da irin abin da yake aikatawa.”}

DAYA DAGA CIKIN SAKONNIN AYAR:

Yadda za a gwada wasu a cikin al’amarin yin biyayyah shi ne a gaya musu su yi abu ba tare da an bayyana musu me zai biyo bayan sun yi wannan aikin ba, sai a bar su a ga shin za su yi ko ba za su yi ba? Kada ma a dage lallai sai sun yi. A sirranta komai da komai dake ciki don a ga idan a yin kansu ne, shin za su yi ne ko ba za su yi ba… shin za su yi maka biyayyah ne ko kuma wani abu na daban ne za su yi. Shin suna fahimtar zurfin zantukanka ne ko kuma dai kawai suna wajen ne kamar gumaka. Shin suna yin hakuri su ga wani sirri ne kunshe bayan sun yi maka biyayyah, ko dai kawai sharholiya ce a gabansu.

Maganar gaskiya idan sun san yin wannan abu da rashin yin hakan zai haifar da fa’ida mai yawa ko kuma zai hana asara da bala’o’i masu yawa, to ba za su kasance cikin halinsu na yau da kullun ba, don haka ko dai su nemi amfani ko kuma su guje wa cutarwa. Kuma wanda ya ba da umarnin ba ya son yin umarni ga mai biyayya saboda tsoron kada a yi masa duka ko kuma don a tursasa shi yin biyayya. Yana son bawa ya yi aiki kuma ya daina aiki don shaukin yin biyayya ga ubangiji ne. Kawai don yana son sa ne. Maganar gaskiya, a cikin dukan bayi, bawan da yake ƙauna da biyayya ga ubangiji ya fi shahara a wurin mai duka (ALLAH). Idan haka ta kasance, sannu a hankali zai samu amincewar mai duka (ALLAH). Sannu a hankali umarnonin ALLAH muhimmai kuma na musamman zai damka a hannunsa, zai zamo Ubangji ya yarda da amince masa, sannu a hankali zai zama mai kima da daraja a wajen ALLAH.

A cikin zurfafa dangantaka tsakanin bawa da Ubangiji, wani abu ya taso wanda ya sa labarin ya fi rikitarwa. Bawa ba shi da ikon kansa, kafin nan kuma ALLAH ne yake aiwatar da niyya da nufinsa. To yanzu da ya kasance baki daya iko na shi ne, yana cewa bawa ka yi niyya iri kaza, kada ka yi niyya iri kaza, domin na yi irin aiki kaza, ka kuma kin yin aiki iri kaza! Ba tare da an yi wani karin bayani ba! Idan niyya da nufin bawa ya dace da umarnin Ubangiji, ALLAH zai kula da shi, kuma da sannu zai sanya haske da sirrin ALLAH a cikin ayyukansa. Kuma idan bai dace da umarnin Ubangiji ba, ba zai ga alheri a cikin ayyukansa ba. To wane ne ba tare da shauki da tsoro ba, zai hade da niyyarsa, wane ne kuma ba zai yi ba.

FASSARA DAGA SHAFIN HONAREVELAEE.IR:
Sadiq Aliyu Musa
30032024

Leave a Reply