RASHIN CIKA ALKAWARI
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI
.وَ الَّذینَ هُمْ لِأَماناتِهِمْ وَ عَهْدِهِمْ راعُونَ وَ الَّذینَ هُمْ عَلی صَلَواتِهِمْ یحافِظُونَ أُولئِکَ هُمُ الْوارِثُونَ الَّذینَ یرِثُونَ الْفِرْدَوْسَ هُمْ فیها خالِدُونَ
مؤمنون ۸ تا ۱۱.
ALLAH (S.W.T) Yana fada a cikin littafinSA Mai tsarki, surar MUMIMUNA, daga aya ta 8 zuwa ta 11, cewa:
{8. Kuma wadanda suke masu kiyayewar amanarsu da kuma alkawarinsu. 9. Kuma wadanda suke kiyaye sallolinsu. 10. Wadannan su ne magada. 11. Wadanda suke gadar (Aljannar) Firdausi su kuwa madawwama ne a cikinta.}
DAYA DAGA CIKIN SAKONNIN AYOYIN:
Da za ka tambayi ko wani mutum cewa kana son zama mumini?, ba tare da shakka ba zai ce: “kwarai!”. Da za ka tambayi ko wani mutum cewa kana son Aljannar Firdausi ta zama sakamakonka?, tabbas zai so hakan! A irin wadannan batutuwan ba a samun sabani… ana samun sabani ne a wani wajen na daban… matsalar shi ne kowa yana son zama mumini kuma Aljannah ta zamo makomarsu amma ba su son aikata hali irin na muminai! Suna tunani kawai iya Sallah da Azumin da suke yi shi kenan sun zama muminai! Ba su ji hadisin Imam Sadiq (A.S) da ke cewa daya daga cikin alamomin mumini shi ne cika alkawari… wata kila ma bangaren da Al-Kur’ani ke magana a kai ma ba su karanta ba.
Amma mu san wannan a tsakaninmu, idan mun yi alkawari ba mu cika wa, to ba mu da imani mai yawa da ALLAH (S.W.T)… bai ma kamata mu nemi sakamako da Aljannar Firdausi ba… asali ma imaninmu bai kai wani matakin da idan mun dauki alkawari mu iya cika wa ba… mun san cewa aikin nan da mu ka dauka zuwa wani lokaci ba zai kammalu ba, amma duk da hakan sai mu yi alkawari!!! Sai mu bar mutane da dama suna jiran mu cika alkawari… muna sanya zukata samun fatan cewa lallai za a yi musu aikinsu, amma duk da hakan ba za a cika musu alkawarin ba…
Tun farko ma mun san aikin ba namu ba ne, amma duk da hakan za mu yi alkawari… Dama wasunmu sam ba su san idan an zo yin batun yarjajjeniya akwai bukatar a yi rubutu da sanya hannu ba. Ba mu tsoron daukan alkawari, wannan alkawarin da mun san za ta bi iska ne… kama daga yin alkawuran da zai sanyaya zuciya… zuwa alkawuran da suke karfafa guiwa… duk muna sanya al’umma aiki ne da sanya rai… asali ma ba mu tunanin cewa irin wannan aikin na rashin cika alkawari yana fitar da mu daga da’irar imani!
Yana ba da gadonmu wa wasu su ci… yana lalata mu… da gaggawa mu ke daukan alkawari… wani lokacin da za mu tattaro alkawuran da mu ka yi tsawon shekara, mu ka hada su waje daya mu ka kalle su, za mu ga sun samar da karfin mutane goma da suka fi karfinmu!! Asali ma ba mu da tsari na rayuwa, aiki, iyali, yaya da sauransu… muna yin alkawari ba tare da lissafi da hangen nesa ba… muna yin alkawari… ba tare da kwarewa da iko ba… yadda mu ke yin alkawari kamar imani ne ke karade mu ta bangarori hudu, amma daga karshe mu yi bankwana da Aljannar Firdausi… To ku hankalta…
FASSARAWA DAGA SHAFIN HONAREVELAEE.IR:
Sadiq Aliyu Musa
14032024