You are currently viewing SAKON ALKUR’ANI MAI GIRMA (1)

SAKON ALKUR’ANI MAI GIRMA (1)

ALLAH S.AW.A na faɗa a cikin littafinsa Mai Tsarki cewa:

“(Shiryayyu su ne) Waɗanda suka yi imani sannan zuciyarsu na samun nitsuwa da ambaton (zikiri) ALLAH. Ku saurara! Da ambaton (zikiri) ALLAH zuciya ke samun nitsuwa.” – Surar Ra’ad, aya ta 28.To abun lura a nan shi ne ambaton ALLAH ba kawai a baki ba ne, saboda ɗaya daga cikin abubuwan da ma’anar ayar take nufi shi ne tuna ALLAH ne, amma abun da aka fi so shi ne a dinga tuna ALLAH a kowace hali, musamman ma a halin da za a aikata zunubi.Muhsin Ƙara’ati mai Tafsirin Nuur, ya kawo amfanonin tunawa da ALLAH har guda 8, ga su kamar haka:

1- Tuna Ni’imarsa, yana sanya a yi masa godiya;

2- Tuna ikonsa, yana sanya a yi tawakkali gare shi;

3- Tuna sassaucinsa, yana janyo a so shi;

4- Tuna fushinsa, yana sanya a ji tsoron sa;

5- Tuna girman sa, yana sanya a ƙanƙan da kai a gabansa;

6- Tuna iliminsa dangane da abun da ya faku (ɓoye) da abun da ya bayyana, yana sanya mu zama masu jin kunya a kamewa;

7- Tuna afuwa da karamcinsa, yana janyo samun fata da neman gafara (tuba);

8- Tuna adalcinsa, yana sanya Taƙawa (tsoron Allah) da nisantar munanan Laifuka.

To ta dalilin ɗan Adam yana neman cikakkiyar kamala ne ya sanya ba ya samun gasasshen nitsuwa da komai sai da ALLAH ɗin, domin kowani abu ragagge ne ba cikakke ba in ban da ALLAH.

Shi ya sa za ka ga mutum ya ce in ya samu kuɗi ya more; wato ya samu kamala, amma idan ya samu sai ya ga ba shi ba ne. In har burinsa auren kyakkyawar mace ce, idan ya aura shi ma kwana 2 sai ya tafi neman wani abun na daban. Haka zai ta yi har ya haɗu da ALLAH zuciya ba ta samu natsuwa ba. Amma idan tun farko ya nemi ALLAH ɗin, sai ka ga ya samu natsuwa, ko da bai tara abun duniya ba.

To sai dai wasu masu tafsirin na ganin tuna ALLAH ba iya ka tuna shi ba ne, ya haɗa da ka san cewa yana sane da kai bai manta da kai ba. To wannan zai warware matsalolin da mutane suke faɗa wa ciki, kamar mutum ya ji cewa mutane ba su son shi. Ko kuma an sako shi gaba. To idan ka tuna cewa lallai ALLAH na sane da kai, kuma ba mai iya maka wani abu face ya amince, to sai ka samu natsuwa kuma damuwar da kake ciki ta yaye. Don yanzu ka san a tare da kai akwai Ubangijinka kuma zai shiryar da kai.

Tuna ALLAH ba kawai iya Musulmai ne suka nuna yana sanya nitsuwa ga mutane ba, hatta waɗanda ba su yarda da ALLAH ba irin su Stephen Hawking sun bayyana mutane sun fi samun nitsuwa da addini fiye da kimiyya. Kuma a ganinmu hakan yana da alaƙa ne da buƙatar mutum na samun kamala madauwamiya; wato ALLAH S.A.W.A.

Insha’Allah muna fatan idan ALLAH Ya ba mu iko, za mu ke zuwa muku da irin wannan Saƙon Alƙur’ani Mai Girma a kullum.

ALLAH Ya ba mu shiriya irinta Alƙur’ani Mai Girma.

Aliyu Abubakar Musa
02122024

Leave a Reply